Zamantakewa

Ƙanƙame Al’adu Ne Kaɗai Zai Kawo Ƙarshen Shaye-Shaye – NDLEA

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, Mohammed Buba Marwa, ya bayyana cewar za a iya kawar da harkar shaye-shaye ne kaɗai, idan al’umma suka rungumi girmama dakoki da kyawawan ɗabi’u da ma martaba Al’adu.

Marwa, ya bayyana hakan ne jiya Talata, a babban birnin tarayya Abuja, ya yin da ya ke jawabi a matsayin mai gabatarwa, a taron da cibiyar wayar da kan al’umma kan al’adu ta ƙasa ta shirya.

Marwa, wanda ya samu wakilcin Daraktan sashen rage amfani da ƙwayoyi na hukumar ya bayyan cewar, tallafar matasan ƙasar nan a fannin Ilimi, tare da samar musu da ayyukan yi , abu ne da zai taimakawa yunƙurin yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da matasan suka tsinci kansu a ciki dumu—dumu.

A ƙarshe, Sakataren cibiyar ta NICO, Ado Muhammed Yahuza, ya bayyana cewar cibiyar ta samar da ƙungiyoyin raya al’adu a matakin makarantun Sakandiren da ke faɗin ƙasar nan, domin ƙara wayar da kan al’ummar ƙasar game da martaba al’adu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button