Kafin A Haifi Ubana ma Akwai Doka Saboda Haka Bazan Rena Kotu Ba – Cewar Kahutu Rarara
Mawaƙin Siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya bayyana cewar, ƙarya Masinjan Babbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke birnin Lafia, a jihar Nasarawa ya ke masa, kan batun zuwa da sammaci gidansa, amma Mawaƙin ya bada umarnin hana shi ganinsa.
Rarara, na ƙaryata batun zuwan Masinjan Kotun Ofishi, ko Gidansa domin miƙa masa sammacin ne, a matsayin dalilin da ya hana shi halartar zaman da Kotun ta fara gudanarwa, a yau (Litinin), kan ƙarar da Wani Fitaccen Ɗan Jarida, Alhaji Sani Ahmad Zangina ya shigar da shi, ya na mai miƙa buƙatar Kotun ta sanya a tsare Mawaƙin, kan abin da ya kira da kalaman tunzura al’umma da Mawaƙin ya furta, ta hanyar zargin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da dagula al’amuran ƙasar nan, kafin barinsa karagar mulki, a ya yin wani taron Manema Labarai da ya gudanar, tun a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata, a jihar Kano.
“Ai ni ban sani ba ai, ai ya kamata a ce sai an sanar da ni ne sannan za a min wani abu, ka ga inda na sani ai dole na amsa, ban isa na tsallakewa doka ba, domin ƙasar ma akan doka ta ke. Ban sani ba, amma tunda ka gaya min yanzu, zan sa lauyana ya bincika”, a cewar Rarara, ya yin da ya ke zantawa ta wayar tarho da wakilin Jaridar ATP Hausa.
Da aka ankarar da shi kan batun cewa, Masinjan Kotun ya yi iya bakin ƙoƙarinsa domin miƙa masa takardar sammacin, amma yaƙi karɓa, sai Rararan ya yi martani da cewa, “A’a wallahi ƙarya ya ke yi, a ina ya ganni ?, a ina ya sanni ?. Ai akwai hanyoyi, ina Ofis a Kano; Ina da Gida a Abuja; Ina da Gida a Kahutu, dukka waɗannan Gidajen ina ya kai ?, Domin kowanne gida akwai wakili da za a ce ga takarda an kawo, ko da ba a karɓa ba, za a sanar da ni, ai wata takarda aka kawo maka daga wuri kaza”.
Rashin karɓar takardar sammacin da Mawaƙin ya yi ne kuma, ya sanya Lauyan Mai Ƙara, Barista Muhammad Barde Abdullahi, ya roƙi Kotun da ta sanya a liƙe masa sammacin a ƙofofin gidajensa da ke faɗin Najeriya. Kuma nan take kotun ta amince da wannan buƙata.
Kotun ta sanya ranar, 4 ga watan gobe na Disamba, a matsayin ranar komawa, domin cigaba da sauraron shari’ar.