Labarai

Ƙasa Awanni 48 Kafin Saukarsa, Gwamnan Plateau Ya Naɗa Shugabar Ma’aikata

Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya amince da naɗin Barista Mrs. Rauta Joshua Dakok, a matsayin sabuwar shugabar Ma’aikatan jihar.

Wannan cigaba kuma na zuwa ne, ya yin da ya rage ƙasa da awanni 48 shugaban ya miƙa mulki ga sabon zaɓaɓɓen Gwamnan jihar, Barista Caleb Mutfuwang.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ce dai, ta ayyana Mutfuwang ɗin a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar, ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP.

Sabuwar shugabar ma’aikatan, Rauta Dakok, zata karɓi Aiki ne dai, daga hannun Injiniya Sunday Hyat, wanda ya yi ritaya, daga Aiki, sakamakon riskar shekarun ajiye Aikinsa, da ma ƙarin watanni huɗun da Gwamnan jihar ya yi masa.

Kafin kasancewarta a wannan muƙami kuma, Barista Dakok, ta kammala karatun Digiri a fannin Shari’a (Law), daga Jami’ar Jos, a shekarar 1988, inda ta fara Aiki da Gwamnatin jihar ta Plateau a shekarar 1990 a matsayin lauyar Gwamnati. Ta kuma yi Aiki a ma’aikatu, da hukumomi daban-daban.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button