Ƙasar India Ta Karrama Kwamishan Shari’ar Nasarawa, A Taron CASGC
Shuwagabannin Ma’aikatar Shari’a ta jihar Nasarawa, ƙarƙashin jagorancin Atoni Janar, kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Shuaibu Labaran Magaji, sun kai ziyara ga Gwamna Engr. Abdullahi A. Sule, a fadarsa, da ke gidan Gwamnati.
A ya yin ziyarar kuma, shuwagabannin ma’aikatar sun gabatar da shaidar karramawar Atoni Janar na Jamhuriyyar India, ya bawa Kwamishinan, lokacin taron Lauyoyi da Atoni Janar-Janar (CASGC) na shekarar 2024 da ya gudana, a Vigyan Bhawan, da ke New Delhi, na ƙasar India, ranar 3 ga watan Fabrairun da mu ke bankwana da shi.
Wannan kuma, ba shi ne karo na farko ba, da Jami’an da ke aiki da Gwamnan ke karɓar kyaututtukan karramawa mabanbanta, daga ƙungiyoyi da hukumomi daban-daban, da ke ciki, da wajen ƙasar nan.
Gwamna A.A. Sule na jam’iyyar APC dai, na cikin wa’adin mulkinsa na biyu ne, tun bayan lashe zaɓen Gwamnan jihar, da hukumar INEC ta gudanar, a shekarar 2023 da ta gabata.