Ƙasashen Ƙetare

Ƙasashen Afirka Na Yunƙurin Sasanta Rikicin Ukraine Da Rasha

A ranar Talata ne, Shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, ya sanar da cewar shuwagabannin kasashen Afirka guda shida na shirin kai ziyara zuwa kasashen Ukraine da Rasha, dan ganin sun bada gudunmawarsu wajen shawo kan yakin da ke tsakanin kasashen wanda ya ki ci – ya ki cinyewa.

Ramaphosa ya kuma kara da cewar, tuni shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, da jagoran Ukraine, Zelenskyy su ka amince za su karbi bakuncin shuwagabannin kwamitin tabbatatar da zaman lafiyar na Afirka, a manyan biranen kasashensu.

Kasashen da za su wakilci Afirkan dai sun hadar da, Zambia, Senegal, Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, Uganda, Egypt, da ma kasar Afirka ta kudu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button