Ƙasashen Ƙetare

Ƙetare: Masu Haƙar Gawayi Sun Mutu, Bayan Fashewar Bututun Gas

Akalla leburori 12 ne su ka rasa rayukansu, ya yin da wani ramin hakar gawayi ya rufta, a yankin Kudu Maso Yammacin kasar Pakistan, bayan samun fashewar wani bututun Gas, a yau Laraba.

Fashewar Gas din ta faru ne, a tsakiyar daren da ya gabata, a garin Harnai, da ke yankin Balochistan, inda ya rutsa da dumbin maáikata, kamar yadda guda cikin masu ruwa da tsakin yankin, mai suna Qismatullah Tareen, ta bayyana.

Tawagar masu ceto, sun shafe tsawon saóí su na aikin tseratar da jamaár da su ka rasa ransu, ya yin da kimanin mutane 12 su ka tsira a raye dauke da raunuka, kamar yadda guda cikin maáikatan sashen agajin, mai suna Mohamed Ahmer ya bayyana.

Fashewar Gas din a ramin hakar gawayi da ke Pakistan, da aka fi sani da ‘Bakaken Ramukan Mutuwa’ wato ‘Black Death Holes’a harshen Ingilishi, na yin sanadiyyar rasa ran daruruwan maáikata a duk shekara, a cewar wasu bayanai da kungiyar Kwadago ta duniya ta fitar.

Kungiyar masu hakar maádanai ta kasar ta Pakistan kuma ta koka da yadda maáikatan hakar gawayin ke aiki cikin hadari, ba tare da amfani da kayayyakin kariya, samun horo, da inshorarar rayuwa ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button