Ƙetare: Putin Ya Lashe Zaɓen Rasha A Hukumance
Shugaba mai ci na ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar na shekarar 2024, kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta CEC ta bayyana, a ranar Alhamis.
Sakamakon ƙarshe da hukumar ta CEC ta bayyana, ya yin taron Manema Labarai, ya nuna yadda Putin ɗin ya samu nasarar lashe kaso 87.28 cikin 100 na ɗaukacin ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen.
Inda bayanan da su ka fito, su ka ce kimanin ƙuri’u 76,277,708 aka kaɗa wa Putin ɗin.
Sai kuma ƙuri’u 3,768,470 da aka kaɗa wa Ɗan takarar Community Party, Nikolai Kharitonov, wanda hakan ya bashi nasarar zuwa na biyu, da kaso 4.31 na ɗaukacin ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen.
Sai kuma Ɗan takarar People Party, Vladislav Davankov, da ya samu ƙuri’u 3,362,484 wato kaso 3.85 na ɗaukacin ƙuri’un zaɓen.
A gefe guda, Jagoran jam’iyyar Democratic Party, Leonid Slutsky, ya samu kimanin ƙuri’u 2,797,629, wato kaso 3.2 na jimillar ƙuri’un da aka kaɗa.
Da ta ke jawabi, shugabar hukumar zaɓen ta CEC, Ella Pamifilova, ta ce an samu fitowar al’umma a ya yin zaɓen, wanda har hakan ya kasance zaɓe mafi fitar yawan al’umma a tarihin ƙasar.
Ta kuma ƙara da bayyana cewar, kimanin masu zaɓe miliyan 87.6 ne su ka kaɗa ƙuri’unsu a ya yin zaɓen, wanda hakan ke wakiltar kaso 77.49 na ɗaukacin masu zaɓen ƙasar.
Ana kuma sa ran, za a rantsar da shugaban a ranar 7 ga watan Mayun shekarar da mu ke ciki.