Ƙetare: Shugaban Rasha Ya Karɓi Baƙuncin Shugaban Koriya Ta Arewa
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya karɓi baƙuncin shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, domin tattaunawa a yau Laraba, kan yadda za su samar da makaman da za su kawo ƙarshen takunkuman duniya.
Putin, ya bayyana matukar jindaɗinsa kan ganin Kim Jong Un ɗin, kamar yadda wata tashar Talabajin a jihar Rasha ta rawaito.
Inda wani faifan bidiyo da tashar Talabijin ɗin ta sanya, ya nuna yadda shuwagabannin biyu su ke gaisawa, tare da riƙe hannun juna, a yankin Vostochny Cosmodrome, da ke nesa da gabashin Rasha.
Ya yin da Kim ɗin ya ke Rasha kuma, Sojojin Kudancin Koriya sun bayyana cewar, za a gabatar da gwaje-gwaje dan ganin yadda za a kawo ƙarshen takunkuman.
Ba wannan ne karon farko ba dai, da manya-manyan ƙasashe ke haɗa kai dan magance wata matsala, da su ke jin ta shalle su.