Kiwon Lafiya

Ƙudirin Tilasta Yin Gwajin HIV Kafin Aure, Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalissar Kano

Majalissar Dokokin jihar Kano, ta yi wa ƙudirin dokar da ke neman wajabta yin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki (HIV)), da Ciwon Hanta kafin Aure, karatu na biyu, a zaman da ta gudanar, a jiya.

Ɗan Majalissa Musa Ali Kachako, da ke wakiltar yankin Takai a Majalissar, wanda kuma shi ne ya gabatar da ƙudirin, ya bayyana yadda mutanen jihar da dama ke ƙulla Aure ba tare da yin gwajin cutar HIV ɗin, da sauran cututtuka ba.

A nasa ɓangaren, Aminu Saad, wanda ke wakiltar Ungogo a Majalissar, ya bayyana cewar, tuni Jihohi irinsu Jigawa, Katsina, da Kaduna su ka sahalewa dokar gwajin, da nufin magance matsalolin yaɗuwar cututtuka, a tsakanin al’ummominsu.

Ya kuma ce, a matsayin Kano na jiha mafi yawan al’umma, wajibi ne ta amincewa wannan doka, ta yin gwaji kafin Aure, domin daƙile yaɗuwar cututtuka masu haɗari, irinsu Ciwon Hanta.

Bayan yi wa ƙudirin karatu na biyu ne kuma, sai Shugaban Majalissar, Ismail Falgore, ya miƙa shi ga Kwamitin Lafiya na Majalissar, domin yi masa duba na tsanaki, tare da gabatar da Rahoto cikin makonni 4.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button