Zamantakewa
Ƙudurin Fara Bada Hutu Ga Iyalan Da Aka Yi Wa Mutuwa, Ya Tsallake Karatu Na Biyu
Ƙudurin Dokar, bayar da hutu ga Maáuratan da dayansu ya rasa ransa, ya tsallake karatu na biyu, a gaban Majalissar Wakilai ta tarayya.
Kudurin, wanda Dan Majalissa Saídu Musa Abdullahi, na jamíyyar APC, daga jihar Niger ya gabatar a zauren majalissar, an yi masa take da ‘Kudurin Dokar Bada Hutu Ga Bazawara Mace, Ko Bazawari Namijin da Aboki ko Abokiyar Aurensu su ka mutu, domin shiryawa tunkarar kalubalen da za su fuskanta’.
Kudurin, ya yi tanadin bayar da hutun watanni biyar ga Macen da ta rasa mijinta, ya yin da Mijin da ya rasa tasa matar zai shafe tsawon wata guda, a cikin hutu.
Bayan amincewa da shi, ana sa ran dokar za ta shafi daukacin maáikatan gwamnati, da na masanaántu masu zaman kansu.