Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Janye Ƙudurinta Na Tsunduma Yajin Aiki, Bayan Ganawa Da Gwamnati

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC, sun bayyana janye shirinsu na tsunduma yajin aiki, tare da gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan, da su ka tsara fara gudanarwa, daga gobe (Laraba) 7 ga watan Yunin 2023.

Bayanin janye ƙudurin tafiya Yajin Aikin kuma, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da gamayyar ƙungiyoyin su ka fitar, mai ɗauke da sa hannun Shugaban TUC na ƙasa, Kwamared Injiniya Festus Osifo; Shugaban NLC, Joseph Ajaero; Sai Sakataren ƙungiyar TUC, Kwamared Nuhu Toro, da kuma Babban Sakataren Ma’aikatar ƙwadago, Ms Kachollom S. Daju; Da ma Shugaban Majalissar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Zaman tattaunawar ƙungiyoyin, da Gwamnatin tarayya dai, ya gudana ne, da yammacin ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, bisa ƙoƙarin shugaban majalissar wakilai, Femi Gbajabiamila.

A ya yin zaman tattaunawar kuma, an kafa kwamitin haɗaka tsakanin Gwamnatin da wakilan ƙungiyoyin ƙwadago, wanda zai yi aikin sake duba na tsanaki kan cire tallafin man da Gwamnatin tarayya ta yi, wanda ya jawo tashin farashinsa, dan lalubo hanyoyin da ya kamata a bi, domin aiwatar da shirin ba tare da jikkatar al’umma ba.

Ka zalika, an yi amfani da zaman wajen tattauna matsalolin da su ka addabi fannin Ilimi, da ma yadda za a shawo kansu, dama matsalolin da su ka shafi titunan sufurin motoci, da na jiragen ƙasa, baya ga farfaɗo da matatun man ƙasar nan.

Za kuma a sake tattaunawa tsakanin Gwamnatin tarayyar da ƙungiyoyin NLC da TUC, a ranar 19 ga watan Yunin da mu ke ciki, domin amincewa da waɗannan tsare-tsare, tare da ƙaddamar da kwamitin haɗakar da zai gudanar da aikin.

Kafin cimma wannan matsaya kuma, daman tuni Kotun Ma’aikata, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a, O.Y. Anuwe, ta umarci ƙungiyoyin ƙwadagon da su dakatar da ƙudurinsu na tsunduma Yajin Aiki, har zuwa ranar 19 ga watan Yunin da mu ke ciki, inda za a saurari ƙarar da Gwamnatin tarayya ta shigar a gabanta.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button