Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago Za Ta Cimma Matsaya Game Da Tsunduma Yajin Aiki, A Ranar Talata

Rassan jihohi, da ma ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), na shirin tsunduma Yajin Aiki a ƙasa baki ɗaya, bayan da wa’adin kwanaki 21 da ƙungiyar ta bawa Gwamnatin tarayya na bayar da tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur, ya kawo ƙarshe.

Idan ba a manta ba dai, ko a kwanakin baya, sai da ƙungiyar ta tsunduma Yajin Aikin gargaɗi na tsawon kwanaki biyu, domin tilasta Gwamnatin ta biya mata buƙatunta.

Ka zalika, bayan gudanar da Yajin Aikin na gargaɗi, NLC ɗin ta bada wa’adin kwanaki 21 ga Gwamnatin, domin ta biya mata buƙatunta.

Ya yin da wa’adin na makonni uku ya kawo ƙarshe a ranar Juma’a kuma, NLC ɗin ta shirya gudanar da taron gaggawa da masu ruwa da tsakin ta na ƙasa, da yammacin ranar Talata.

Ana kuma sa ran ƙungiyar za ta bayyana matakin ta na gaba, bayan kammala gudanar da taron.

Ta cikin sanarwar taron, mai ɗauke da kwanan watan, 22 ga watan Satumban da mu ke ciki, Sakatarenta na ƙasa, Emmanuel Ugboaja, ya bayyanawa Shuwagabannin ƙungiyar, Sakatarorinta, da ma Ma’ajin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta cewar, halartar su taron ya na da matuƙar muhimmanci.

Gabanin gudanar da taron kuma, rassan jihohi na ƙungiyar sun bayyanawa Jaridar PUNCH a ranar Asabar cewar, a shirye su ke su shiga a dama da su, idan kwamitin zartarwar ƙungiyar ya ɗauki matakin tsunduma Yajin Aiki, a ranar Talata.

Sai dai, a gefe guda, raɗe-raɗi na bayyana yiwuwar Gwamnatin tarayya za ta zauna da ƙungiyar a ranar Litinin, gabanin ɗaukar matakin tsunduma Yajin Aikin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button