Tsaro

Ƙungiyar Ƴan Jaridu Masu Rajin Tabbatar Da Zaman Lafiya Za Ta Haɗa Guiwa Da Gwamnatin Kaduna

Hukumar tabbatar zaman lafiya ta jihar Kaduna, ta bayyana godiyarta ga Ƙungiyar Ƴan Jaridu masu Rajin tabbatar da zaman lafiya ta NPJ, bisa gagarumin ƙoƙarinta wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin alúmmar jihar, da ma ƙasa baki ɗaya.

A ya yin, tattaunawar da su ka gudanar a jihar Kaduna, shugaban hukumar tabbatar da zaman lafiya na jihar, Bishop Idowu Fearon, ya yabawa ƙungiyar ta NPJ bisa namijin ƙoƙarinta wajen yaƙar labarun ƙarya, da batutuwan da ka iya rarraba kan alúmma ta fuskar siyasa,da shugabancin addinai.

Bishop Fearon, ya kuma jaddada irin rawar da Ƴan Jarida su ke da ita, wajen haɓɓaka zaman lafiya , ya na mai buga misali da ɓoye labarun da ka iya jawo cecekuce ko tashe-tashen hankula.

Da ya juya kan ƙalubalen da jihar ta ke fuskanta kuwa, Shugaban ya buƙaci haɗin kan ƙungiyar Ƴan Jaridun ta NPJ, wajen ganin an shawo kan matsalolin ƴan bindiga, satar mutane, faɗace-faɗace da rikicin addinai, da ma labarun ƙarya.

Ya kuma, roƙi Ƴan Jaridu da su kasance masu bin ƙwaƙwƙwafi da nufin daƙile yaɗuwar labarun ƙarya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button