Ilimi

Ƙungiyar Ɗaliban Ɓagwai, Ta Yi Allah-Wadai Da Yadda Mahukunta Ke Watsi Da Harkar Ilimi

Ƙungiyar Ɗaliban ƙaramar hukumar Ɓagwai, da ke jihar Kano, ta yi Allah-Wadai da yadda Mahukunta, ke nuna halin ko inkula game da harkokin Ilimi, a ƙaramar hukumar.

BALSA, ta bayyana wannan mataki ne, ta cikin wata sanarwa da Jami’in Bincikenta (Auditor General), kuma shugaban kwamitin Ilimi na ƙungiyar, Comrade Abdullahi Usman Wakili, ya aikowa Jaridar Rariya Online, da safiyar Alhamis.

Sanarwar kuma, ta ƙara da fito da halin ƙaƙanikayin da Ilimi ya tsinci kansa a ƙaramar hukumar, da ma yadda kowanne ɓangare na mahukunta ke kawar da kai, game da batun.

Inda, ƙungiyar ta BALSA, ta buƙaci masu ruwa da tsakin ƙaramar hukumar da su haɗa hannu waje guda, dan ganin an haɓɓaka fannin na Ilimi.

Ka zalika, ƙungiyar ta ƙara da roƙon mahukuntan kan su sa ɗamba, ta hanyar fara biyawa Ɗalibai kuɗaɗen Jarrabawar neman shiga manyan makarantu (JAMB UTME), ta wannan shekarar (2024).

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button