Labarai

Ƙungiyar Lauyoyi Ta Buƙaci Kotu Ta Sauke Ministar Al’adu

Ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa (NBA), ƙarƙashin sashenta na kula da dokokin cigaban al’umma, NBA-SPIDEL, ta buƙaci Babbar Kotun tarayya, da ke Abuja, da ta kori Ministar Raya Al-adu, Hannatu Musawa, daga kan muƙaminta, bisa zarginta da yin karantsaye, ga dokar hidimar ƙasa (NYSC).

Ta cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/05/90/2024, NBA ɗin ta roƙi NYSC da ta soke takardar shaidar da aka damƙawa, Hannatu Musawa, tare da Shugaban Kennis Music, Kenny Ogungbe.

Idan za a iya tunawa dai, tun a watan Augustan shekarar da ta gabata ta 2023, ƙungiyoyin cigaban al’umma, da na kare haƙƙoƙin ƴan Adam, da ma na Marubuta, sun zargi Hannatu Musawa ɗin, da ɗarewa kujerar Minista, ya yin da ta ke tsaka da gudanar da hidimar ƙasa (NYSC) ta tsawon shekara guda.

NYSC, ta kuma tabbatar da cewar, Musawa ɗin tana tsaka da hidimar ƙasa a wancan lokaci, duk da kasancewarta mai riƙe da muƙamin gwamnati, kuma wacce ta haura shekaru 30.

Ka zalika, a watan Oktoban shekarar ta 2023, shi ma Mr Ogungbe ya wallafa hotonsa sanye da kayan hidimar ƙasa, ya na mai cewar ya kammala hidimtawa ƙasarsa ya na da shekaru 53.

Inda NBA ɗin ta ce, babu shakka samarwa waɗannan mutane biyu takardar kammala hidimtawa ƙasar, abu ne da ya ci karo, da dokar NYSC (Act Cap N84.LFN 2024).

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button