Labarai

Ƙungiyoyin Ƙwadago Za Su Tsunduma Yajin Aiki, Da Zarar An Rantsar Da Tinubu

Ƙungoyin ƙwadago na NLC, da TUC, sun bayyana shirinsu na tsunduma yajin aiki, a watan Yuni, dan bayyana adawarsu da matakin da Gwamnatin shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, za ta ɗauka, na cire tallafin man fetur.

Sai dai, dukkannin ƙungiyoyin sun kafa sharaɗin cewar, za su haƙura da gudanar da yajin aikin, ida har Gwamnati za ta farfaɗo da matatun man ƙasar nan da su ka durƙushe, tare da bayar da alawus ga ƙananun matatu.

A cewar ƙungiyoyin kuma, gaza aiwatar da hakan, tare da ɗaukar kishiyarsa, wato cire tallafin mai, zai haifar da tsundumar ƙungiyoyin yajin aiki, tare da gudanar da gagarumar zanga-zanga.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari dai, ya bayyana cewar, za a cire tallafin man ne, kafin ƙarewar zangon mulkinsa, a ranar 29 ga watan Maris ɗin 2023.

Sai dai, da ya ke martani, Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi na ƙasa (NULGE), Hakeem Ambali, ya ce suma tasu ƙungiyar bata goyon bayan sutale tallafin man.

Ambali, wanda shi ne ma’ajin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ya bayyana hakan ne, a wata tattaunawa, da ya gudanar da jaridar PUNCH, a babban birnin tarayya Abuja.

Shi ma shugaban ƙungiyar Ƙwadago ta TUC na ƙasa, Titus Amba, ya ce su na tare da matsayar NLC kan batun cire tallafin man.

Sai dai, ya shawarci Gwamnatin mai zuwa, ta Tinubu, da ta ɗora da bada tallafin, domin zama lafiya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button