Ƴan Arewa Ba Su Da Damar Ƙorafi Kan Naɗe-Naɗen Tinubu – Zauren Matasan Arewa
Zauren Shuwagabannin Matasan Arewa (NYLF) ya bayyana cewar, Jama’ar Arewa ba su da damar yin ƙorafi kan naɗe-naɗen da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Wannan martani kuma na zuwa ne, bayan da wasu daga cikin shuwagabannin yankin na Arewa su ka fara ƙalubalantar shugaba Tinubun, bisa zarginsa da fifita yankin Kudu Maso Yamma, wanda shi ne yankin da ya fito, akan sauran ɓangarorin ƙasar nan, a cikin muƙaman da ya naɗa.
Cikin waɗanda ke ƙalubalantar Tinubun kuma, akwai Malamin Addinin nan, Ahmad Gumi, wanda shi ma ya zargi shugaban da naɗa Kiristocin Kudu akan manyan muƙamai masu maiƙo a ƙasar, inda har ya ke cewa muddin za a tafi a haka, to shugaban ba zai sake lashe zaɓe a karo na biyu ba.
Malamin ya kuma zargi Tinubun da yin amfani da yankin Arewa wajen ɗarewa karagar shugabancin ƙasar nan, domin cimma muradinsa na tarwatsa haɗin ka yankin ta fuskar siyasa.
Sai dai, da ya ke zantawa da Manema Labarai, a birnin Abeokuta na jihar Ogun, shugaban zauren NYLF, Elliot Afiyo, ya ce ai Tinubu ma ya ɗinke tazarar da ake da ita a fagen raba muƙamai ne, idan aka yi duba da abin da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya gadarwa ƙasar.
Inda ya ce a zamanin Buhari, kaso 80 na dukkannin muƙaman da aka bayar daga yankin Arewa su ka fito, kawai kaso 20 ne aka bawa yankin kudu.