Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Ƙauyukan Zamfara 4 Ƙawanya, Tare Da Awon Gaba Da Mutane 150
Wasu Ƴan Bindiga sun yi awon gaba da mutane 150, wanda mafi yawansu Mata ne da Ƙananan Yara, a ƙaramar hukumar Maru, ta jihar Zamfara, a ranar Juma’a.
Sun kuma hallaka mutum guda, a ya yin harin nasu wanda ya shafe tsawon sa’o’i, kamar yadda mazauna yankin su ka bayyana.
Hakan kuma na zuwa ne, mako guda, bayan sace wasu mutane 17 da aka yi, a ƙauyen Ruwan Ɗorawa, da ke ƙaramar hukumar ta Maru.
Ƴan bindigar dai, sun kai hari ne ƙauyuka huɗu, da su ka haɗarda Mutunji, Kwanar-Dutse, Sabon-Garin Mahuta, da Unguwar Kawo, a ya yin sumamen nasu na baya-bayan nan.
A zantawarsa da Manema Labarai, wani mutum da ke zaune a Mutunji, guda daga cikin ƙauyukan da aka kaiwa harin, ya ce ƴan bindigar sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 9 na daren Juma’a, inda bayan nan ma su ka haɗa da wasu ƙauyukan guda uku.
Shima wani mazaunin garin, wanda ya buƙaci a ɓoye bayanansa, ya ce su na zaton Ƴan Bindigar daga tawaga ɗaya su ke, kawai dai sun raba kansu ne gida huɗu, domin samun damar farmakar ƙauyukan baki ɗaya.