Ƙasashen Ƙetare

Ƴan Jaridu Sun Dakatar Da Aiki, Ya Yin Da Ake Gudanar Da Zanga-Zanga A Ƙasar Guinea

Akasarin kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu da ma waɗanda ke gudanar da ayyuka a kafafen sada zumunta na zamani sun shiga yajin Aikin kwana guda, kan alámuran yaɗa labarai a ƙasar Guinea, hakan kuma na zuwa ne bayan yunƙurin daƙushe ƴancin kafafen yaɗa labaran da hukumomin ƙasar ke yi.

An kuma sanar da gudanar da zanga-zangar ne tun a ranar Litinin, bayan da gwamnatin mulkin soji da ke jagorantar ƙasar ta garƙame wasu tashoshin Radio guda biyu, mallakin kamfanin yaɗa labarai na Afric Vision Group, baya ga taƙaita amfani da fitattun shafukan yanar gizo, da ma kafafen sada zumunta da gwamnatin ta yi, da ma ikirarin cigaba da garƙame dukkannin wata kafar yaɗa labarai da ta yi yunƙurin tarwatsa haɗin kan ƙasa.

Sai dai, Gwamnatin ƙasar ta musanta wannan zargi na rufe kafafen yaɗa labaran mallakin Afric Vision, da ma toshe shafukan intanet.

A halin da ake ciki kuma, fararen a ƙasar na cigaba da kira ga gwamnati da ta martaba ƴancin yaɗa labarai, kamar yadda kundin dokokin ƙasar ya yi tanadi.

Ƙasar ta Guinea dai, na cigaba da kasancewa a ƙarƙashin mulkin soji ne tun shekarar 2021, bayan ɓarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button