Kasuwanci

Ƴan Kasuwar Albasa Sun Koka, Kan Ƙarancin Wurin Ajiya

Ƴan kasuwar Albasa sun koka kan yadda ƙarancin ingantattun wuraren ajiya, a kasuwar Gun-Dutse, da ke ƙaramar hukumar Kura, ta jihar Kano, ke cigaba da jawo musu tafka asara, sakamakon ƙarancin wuraren ajiyar amfanin, da ma rashin wadataccen faɗin ƙasa.

Sun kuma ce hakan na taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar albasoshin nasu da su ka samar, wanda hakan ke haifar da gaza samun riba, a harkokin kasuwancinsu.

Wani ɗan kasuwa a kasuwar, ya bayyana cewar, Albasar da ake sayarwa a kasuwar ta yi shura a fagen inganci, da ma ɗanɗano, a cikin ƙasar nan, da ma ƙasashen ƙetare.

Sai dai ya koka, kan yadda ya ce a lokacin damina, su na ƙirga gagarumar asara da ta kai ta miliyoyin Naira, saboda rashin ingantaccen wurin ajiya.

Ya kuma ƙara da bayyana buƙatar kasuwar, ta samar mata da wadataccen filin da zai iya wadatar da adadin mutanen da ke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar, da ma masu siyayya, duba da yadda filin kasuwar ya yi matsi, a halin yanzu.

A nasa ɓangaren, wani babban bafataucen Albasa, a kasuwar ta Gun-Dutse, Bala Ibrahim, ya ce akwai buƙatar gwamnati ta taimaki ƴan kasuwar ta hanyar samar musu da wuraren ajiya na zamani.

Gun-Dutse dai, fitacciyar kasuwa ce, da ke jan hankalin masu sayayya, daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan, da ma maƙwabtan ƙasashe, kamar Nijar da Kamaru.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button