Ƴan Kasuwar Lagos Sun Koka Kan Yawan Karɓar Haraji
Ƴan kasuwa daga kasuwanni daban-daban na jihar Lagos, musamman ma kasuwar Balogun, da ke ƙaramar hukumar Lagos Island, sun koka kan yawaitar harajin da Gwamnatin jihar ke karɓa daga wurarensu, ba ya ga yi musu barazana.
Da su ke zantawa da Manema Labarai, wasu daga cikin ƴan kasuwar ta Balogun, sun yi iƙirarin cewar ana tilasta musu biyan harajin Naira Dubu 50 cikin kowanne watanni shida, ya yin da sauran ƴan kasuwar ke biyan sama da Dubu 100 a shekara guda.
Ƴan kasuwar sun kuma ƙara da bayyana cewar su na biyan harajin Naira 700 a kowacce rana, inda ake barazanar korarsu daga wuraren gudanar da sanaóín nasu a duk lokacin da su ka yi yunƙurin bijirewa biyan harajin.
Da aka tuntuɓe shi, Babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Gboyega Akosile, ya tabbatar da aukuwar hakan, ya na mai jaddada cewar, wajibi ne dukkannin wani wanda ya ke aiki a jihar ya biya haraji, ko da ya kasance ƙaramin ɗan kasuwa, ko mai babban kanti.