Ƴan Majalissa Sun Buƙaci Ma’aikatar Masana’antu Ta Mayar Da Kuɗaɗen COVID-19
Kwamitin kula da al’amuran jama’a na Majalissar Wakilai, ya umarci Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci, da bunƙasa hannun jari ta tarayya, da ta mayar da Naira biliyan 75 ɗin da aka ware mata, na kuɗaɗen COVID-19.
Buƙatar hakan kuma ta zo ne, bayan ƙudirin da Ɗan Majalissa, Bassey Akiba, na jam’iyyar Labour Party, daga jihar Cross River ya shigar a gaban majalissar, sakamakon gaza bayyanar shuwagabannin Ma’aikatar, a gaban Majalissar, yau (Alhamis), domin kare kansu, dangane da binciken da Majalissar ke gudanarwa.
A baya-bayan nan dai, Majalissar ta gayyaci kimanin ma’aikatu, sassa da hukumomi 59, domin bayyana a gabanta, a wani mataki na neman jin ba’asin kuɗaɗen da ake zargin an kashe ba bisa ƙa’ida ba, a lokacin da ake fafutukar daƙile annobar Coronavirus, da ta addabi duniya.
Tun da farko kuma, an sanya ranar Laraba, 17 ga watan Janairu ne, domin gudanar da zaman jin ba’asin, inda daga baya aka sauya ranar zuwa Alhamis.
A ya yin zaman majalissar ne kuma, aka amince da ƙudirin tilastawa ma’aikatar dawo da kuɗaɗen da aka ware mata.ɗsauraron