Labarai

Ƴan Majalissar Wakilai Sun Buƙaci Gwamnati Ta Rabawa Talakawan Najeriya Hatsi

Membobin majalissar wakilai, sun yi kira ga Gwamnatin tarayya, da ta gaggauta buɗe rumbunan adana hatsin ƙasar nan, tare da fito da shi, domin rabawa Talakawa masu ƙaramin ƙarfi.

Inda ƴan majalissar su ka ce, hakan zai taka gagarumar rawa matuƙa, wajen fatattakar fatara, da yunwa.

Wannan kira kuma, ya biyo bayan ƙudirin da Ɗan Majalissa mai wakiltar Ifo da Ewekoron jihar Ogun, Ibrahim Isiaka, ya shigar a gaban Majalissar.

Da ya ke jagorantar tafka muhawara kan ƙudurin, Isiaka ya haskawa ƴan majalissar kan yadda tsadar rayuwa ke cigaba da tsananta ga al’ummar ƙasar nan, ya na mai buga misali da yadda farashin siminti ya yi tashin gwauron zabi.

Bayan amincewar majalissar kuma, Majalissar ta ƙara da kira ga Gwamnatin tarayya da ta bunƙasa tsare-tsarenta na Samar da wadataccen Abinci.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button