Ƴan Mata 15 Sun Mutu, A Hatsarin Kwale-Kwale
Sama da yara mata 15 ne su ka rasa rayukansu, bayan da wani kwale-kwale ya yi hatsari, a kauyen Dandeji, da ke karamar hukumar Shagari, ta jihar Sokoto.
Rahotanni sun kuma bayyana cewar, yan matan na kan hanyarsu ne ta zuwa dajin da ke kusa da kauyen nasu domin samo itacen girki, ya yin da jirgin ya tuntsure, da safiyar ranar Talata.
A cewar wasu shaidun gani da ido dai, sama da yara mata 40 ne akan jirgin ruwan, a lokacin da lamarin mara dadi ya auku. Wani mazaunin yankin, mai suna, Muhammad Ibrahim, ya ce gawarwaki 15 aka samu nasarar zakulowa, ya yin da ake cigaba da laluben sauran wadanda lamarin ya rutsa da su. A nasa bangaren, shi ma shugaban karamar hukumar ta Shagari, Aliyu Abubakar, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce tuni aka fara shirye-shiryen binne gawarwakin mamatan.