Ƴan Najeriya Sama Da Miliyan 90 Ne Ke Cikin Duhun Duƙununu – Tinubu
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce duk da cefanar da fannin wutar lantarkin da aka yi tun sama shekaru 10 da su ka gabata, har yanzu sama da ƴan Najeriya miliyan 90 ne ke cikin duhun duƙununun rashin wutar lantarki.
Shugaban ya bayyana hakane, ya yin da ya ke gabatar da jawabi, a taron cikar kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasa (NESI) shekaru 10, da ya gudana jiya, a babban birnin tarayya Abuja.
Tinubu, ya kuma koka da yadda wutar da ƙasar nan ta ke iya samarwa bata wuce kaso 15 na abinda ake buƙata, wanda hakan ke tilastawa kamfanoni da gidaje amfani da Injinan janareta.
Shugaban ƙasar, wanda ya samu wakilcin mai bashi shawara na musamman kan inganta hasken wutar lantarki, Sadiq Wanka, ya ce a yanzu haka, kaso 40 na wutar da ake amfani da ita a ƙasar nan, ana samar da ita ne daga injinin janareto.
Ka zalika ya koka, kan yadda ake gaza biyan kuɗaɗen wutar da ake amfani da ita, bayan da ya ce kaso 60 na kuɗin kowanne kWh guda na wuta kawai ake iya biya, musamman ma bayan da darajar Naira ta karye.
Shugaban ya kuma, haska buƙatar da ke akwai ta sake fasalta yadda ake biyan kuɗin wuta a ƙasar, domin tabbatar da cewa, kowa na biyan kuɗin abin da ya sha ne, wanda hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa sanya hannayen jari a fagen, tare da farfaɗo da shi.
A nasa ɓangaren, Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce ba za su sauyawa kamfanoni lasisin da aka basu tun lokacin da aka mayar da wutar lantarki zuwa hannun ƴab kasuwa a wannan shekara ta 2023 ba, har sai kamfanonin sun cika wasu sharuɗɗa.
Ministan, ya kuma ce har yanzu megawatt 4,000 na lantarki kawai Najeriyar ke iya samarwa, inda ya ce a ganinsa cefanar da fannin da aka yi ga kamfanoni masu zaman kansu, ba shi ne abin da ya dace da ƙasar ba, domin kamata ya yi a ce Gwamnati bata tsame hannunta daga ciki ba.
Ya kuma kafa hujja da cewar, masu sanya hannayen jari masu zaman kansu, ba za su iya haƙurin rainon fannin, kafin fara cin moriyarsa kamar yadda Gwamnati za ta yi ba.