Ƴan Najeriya Za Su Dara, Bayan Tada Komaɗar Tattalin Arziƙi – Ministan Labarai
Ministan yada labarai da wayar da kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewar al’ummar Najeriya ba za su yi ladamar hakuri da sadaukarwar da su ka yi ba, ta fuskar farfado da tatalin arzikin kasa, da sabuwar gwamnatin kasar nan ke yi.
Da ya ke jawabi, jiya a babban birnin tarayya Abuja, ya yin kaddamar da bikin membobin Makarantar bada horo kan hulda da jama’a, ya bayyana cewar, kokarin tada komadar tattalin arzikin da gwamnatin tarayya ke yi, ba abu ne da zai yiwu salim-alim ba, amma muddin lamarin ya kammala, to babu shakka al’ummar Najeriya za su dara.
Ministan ya kuma roki al’umma da su kara hakuri, su kuma bawa Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu lokaci, dan ganin rawar da za ta taka.
Ya kuma bayyana yadda gwamnatin mai ci, ta cimma dumbin nasarori a wasu manyan bangarori na tattalin arziki, cikin kankanin lokacin da ta tsinci kanta akan karagar mulki.