Labarai

Ƴan Sanda Sun Ƙara Daƙume Likitoci 2 A Plateau, Bisa Zargin Cefanar Da Sassan Ɗan Adam

Rundunar Ƴan Sandan jihar Plateau, ta sake kama wasu Likitoci guda biyu, waɗanda ke da alaƙa da binciken da hukumar ta ke gudanarwa akan Noah Kekere, na cirewa, tare da cefanar da ƙodar wata mara lafiya.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, shi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ranar Talata, a birnin Jos.

Alabo, ya bayyana cewar, ƙarin waɗanda ake zargin, da shi Dr. Kekere, a yanzu haka su na tsare a komar hukumar, ya yin da a ke cigaba da gudanar da bincike.

Idan mai karatu bai manta ba dai, a makon da ya gabata ne, Jami’an ƴan sanda su ka yi ram da Dr. Kekere, bisa zarginsa da cefanar da ƙodar wata mata wacce ya cire, a ya yin da ya ke yi mata Tiyata.

A nata ɓangaren, ƙungiyar Likitoci ta ƙasa (NMA) reshen Jihar ta Plateau, ta nisanta kanta da Kekere, ta na mai cewar bincike ya tabbatar da cewar ba Likita bane shi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button