Ƴan Sanda Sun Ci Zarafin Ƴan Jaridu, Tare Da Hana Su Shiga Kotun Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Kano
Ƴan Jaridun da su ka yi dandazo a harabar Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan Kano, wacce ke shirin yanke hukunci a yau, su na cikin matsanancin hali, bayan da Jami’an ƴan sanda su ka hana su shiga Kotun, tare da cin zarafin da dama daga cikinsu.
Daga cikin waɗanda Jami’an ƴan sandan su ka ci zarafi dai, akwai Wakilin BBC Hausa, Zahraddeen Lawal, da na Daily Trust, Salim Umar Ibrahim.
Jami’an Ƴan Sandan sun buƙaci Ƴan Jaridu da su yi nesa da harabar Kotun da aƙalla mita 10, a ya yin da su ke yunƙurin hakan ne kuma, sai wasu daga cikin Jami’an su ka fara farmakarsu, bisa zargin wai su na ɗaukarsu a hoto.
Da dama daga cikinsu dai, sun cukumi wakilin BBC, inda su ka yi yunƙurin ƙwace wayarsa daga Aljihun da ya jefata, ya yin da shi ma wakilin Daily Trust ya fuskanci irin wannan barazanar ta ƙwace waya, wanda har ya kai ga lalata Screen ɗinta.