Labarai

Ƴan Sanda Sun Garƙame Jami’an NDLEA Da Civil Defence, Bisa Zargin Cin Zalin Jama’a

Rundunar ƴan sandan jihar Imo, ta garƙame wasu Jami’an hukumar hana sha da fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) guda uku, tare da na hukumar kare fararen hula (NSCDC), bisa zarginsu da cin zarafin Jama’a, a Jihar.

Kakakin rundunar, ASP Henry Okoye ne ya bayyana hakan, ya yin da ya ke zantawa da Manema Labarai, ranar Talata, a Owerri.

Daga cikin waɗanda aka daƙume ɗin bisa zargin aikata irin wannan laifi, har da wani Jami’in ɗan sanda, mai shekaru 37, da ke da muƙamin Sufeto.

Kakakin ya ce, an kama dukkannin waɗan nan Jami’ai ne, bisa zargin cin zalin fararen hular da basu ji ba, ba su gani ba, musamman ma Matasa, a Owerri, ta hanyar amfani da Injinan cirar kuɗaɗe na POS.

“Su na amfani da POS, tare da ƙwatar Wayoyin Jama’a da bincikasu, wanda hakan ke jefa Jama’a cikin matsu”, a cewarsa.

Okoye, ya kuma tabbatarwa da Al’umma cewar, za su gurfanar da waɗanda ake zargin, a gaban Kuliya, da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button