Ƴan Sanda Sun Kama Mahaifiyar Da Ta Yi Yunƙurin Cefanar Da Jaririnta
Rundunar ƴan sandan jihar Lagos, ta ce ta samu nasarar kama wata Mahaifiya, tare da Mace guda, bisa zarginsu da yunƙurin cefanar da wani jariri, mai watanni tara kacal, a duniya.
Mai magana da yawun rundunar, SP Banjamin Hundeyin ne, ya tabbatar da cigaban, ta cikin wani jawabi da ya fitar, a ranar Asabar.
Inda ya ce, Jami’an sashen RRS na rundunar ne su ka samu nasarar dakume matan, a ranar Juma’a.
Ya kuma ce, an samu nasarar tarwatsa shirin sayar da jaririn ne, a yankin Oshodi, bayan da aka kama dillalin da ke shiga tsakanin mai sayen, da Uwar jaririn, Oge Okolie, mai shekaru 25.
Mahaifiyar Jaririn, Maria Ahmadu, mai shekaru 26 ce dai, ta miƙa yarinyar ga Oge, domin cefanarwa.
Kuma tuni, aka miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashen kula da sha’anin jinsi, domin faɗaɗa bincike.