Ƴan Sanda Sun Kama Mutane 15 Da Ke Cikin Halin ‘Yunwa’, Bisa Zargin Fasa Rumbun Abincin Gwamnati
Rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana yadda ta samu nasarar daƙume mutane 15 da ake zargi da hannu wajen fasa rumbun ajiyar abinci, na hukumar raya babban birnin tarayya Abuja (FCTA).
Kakakin rundunar ƴan sandan na Abuja, SP Josephine Adeh, ita ce ta bayyana hakan, ta cikin wani jawabi da ta fitar, ranar Lahadi, a babban birnin tarayya Abuja.
Ta kuma ce, daga cikin waɗanda ake zargin har da masu gadin rumbun guda biyu, an kuma samu nasarar ƙwato buhun masara guda 26 daga hannun waɗanda ake zargin, da ababen Hawa guda biyar, tare da kwanon rufi na aluminium.
Idan za a iya tunawa dai, a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris ne, wasu fusatattun ƴan Najeriya, da ke cikin halin yunwa, su ka fasa rumbun adana abinci na hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, da ke yankin Tasha, tare da wawashe abinci, da sauran kayayyakin da ke ƙunshe a makeken rumbun.
Rundunar ƴan sandan ta kuma ce, tuni zaman lafiya da kwanciyar hankali su ka dawo a yankin da lamarin ya faru.