Zamantakewa

Ƴan Sanda Sun Kama Mutum 3 Bisa Zargin Satar Kayan Kiɗan Coci

Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Delta, sun kama wasu mutane da ake zargi da tsallakawa cikin Coci da daddare, tare da wawashe kayayyakin kiɗan da ake amfani da su, a cocin.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Bright Edafe, ya bayyana cewar, Jami’an ƴan sanda sun shiga aikin lalubo waɗanda ake zargin ne a lungu da saƙunan jihar, tun bayan da aka shigar musu da ƙorafin sace kayayyakin kiɗan Cocin, da ke Orerokpe, cikin helikwatar ƙaramar hukumar Okpe.

Mutum biyu kuma rundunar ta samu nasarar fara cafkewa, kafin sake cika hannu da ragowar ɗayan.

“Mun gano su ne, bayan da guda daga cikinsu mai suna, Patrick, ya sanya hoton Amplifier ɗin da ke cikin kayayyakin da su ka sata, a shafinsa na Facebook, ya na shirin sayarwa. Nan ne kuma Jami’anmu su ka yi masa ƙofar rago, ta hanyar cewa za su siya, inda ya kwatanta musu cewar su same shi a shatale-talen Effurun.

“Bayan cafke Patrick mai shekaru 36 ɗin ne kuma, sai mu ka samu nasarar kama Alex, mai shekaru 45 shi ma”.

Bayan zurfafa bincike kuma, an gano cewar, ɓarayin sun gwanance matuƙa, wajen iya ɓalle Coci, shago, ko gida, su kuma runtuma sata.

Kayan da aka samu nasarar ƙwatowa a hannun ɓarayin, sun haɗarda manyan lasafiƙoƙi guda 20, Injinan Janareta 3, Amplifier 15, Madannai (Keyboards) 4, Amplifier masu amfani da lantarki 12, Fankokin ƙasa guda 10, Saitin kayan kiɗa mai gangs guda 1, Algaita 1, Mic 1, Firji 2, Talabijin ɗin bango 2, Home Theatres 2, Injin Wanki 1, Stabilizer 3, Handsaws 3, Clipper ta aski 1, Injin Gashi (Microwave) 1, Ƙaramin Oven 1, da kuma Silindar Gas ita ma guda 1.

Ɓarayin kuma, na tsare a hannun Jami’an rundunar ta ƴan sanda, inda ake shirin gurfanar da su a gaban kotu, da zarar an kammala bincike.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button