Ƴan Sanda Sun Kama Sufeton Bogi
Rundunar ƴan sanda, ta samu nasarar daƙume wani mutum da ke basaja, a matsayin sufeton rundunar, a jihar Lagos.
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da daƙume sufeton na bogi, ga Manema labarai, a ranar Talata.
Inda Hundeyin ɗin ya ce, wanda ake zargin ya na amfani da wata Motarsa ne marar rijista, wajen yin hada-hadarsa, a yankin Ikorodu, na jihar Lagos.
Ya kuma ce, tawagar su da ke gudanar da zagayen atisaye ce, ta fara zargin cewa Sufeton na bogi ne, Inda su ka tsayar da shi domin ya bayyana musu shaidar kasancewar ɗansanda, a ranar Lahadi, da misalin ƙarfe 10:22 na dare, amma ya gaza yin hakan.
Wanda hakan ne ya sanya su ka daƙume shi, kuma a yanzu haka, ya na tsare a komar ƴan sanda.
Za kuma, a gurfanar da shi a gaban Kotu, domin girbar abin da ya shuka, da zarar an kammala bincike.