Ƴan Sanda Sun Tarwatsa Ɗaliban ATBU, Ya Yin Da Su Ke Tsaka Da Zanga-Zangar Nuna Fushi Kan Hallaka Ɗan Uwansu
An fuskanci hargitsi a reshen Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, da ke Yelwa, a jihar Bauchi, bayan da Jami’an ƴan sanda su ka bankawa Ɗaliban da ke gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kashe ɗan uwansu barkonon tsohuwa.
Idan za a iya tunawa dai, wasu masu ƙwacen waya ne, su ka kashe Ɗalibin ajin ƙarshe a Jami’ar mai suna, Joseph Agabaidu, ta hanyar burma masa wuƙa, ya yin da su ke yunƙurin karɓe wayarsa.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewar, Ɗalibin wanda ke aji na biyar, a sashen nazarin ma’adanan ƙasa da duwatsu (Geology), ya na kan hanyarsa ne ta komawa ɗakin kwanan ɗalibai, da ke kusa da kasuwar Yelwan Tudu, a Unguwar ta Yelwa, ya yin da aka kawo masa harin, da misalin ƙarfe 7 na Magribar, ranar Asabar.
Nan da nan kuma aka garzaya da shi Asibiti, bayan soka masa wuƙar, wanda a can ne yace ga garinku nan.
Hakan kuma ya sanya Ɗaliban gudanar da zanga-zangar lumana, a farfajiyar makarantar, domin nuna fushinsu, amma Jami’an tsaro su ka dakatar da su da ƙarfin tuwo.
Har yunƙurin fita waje dai, sai da ɗaliban su ka yi, amma Jami’an tsaron su ka hanasu.
An garƙame ƙofar shiga makarantar, ya yin da Jami’an ƴan sanda su ka tilastawa Ɗaliban komawa ciki. Gaza komawar ne ma ya sanya, Jami’an su ka yi wa Ɗaliban ruwan barkonon tsohuwa, wanda hakan ne ya tilasta musu komawa ciki.
An dai hangi yadda Ɗaliban ke ta toshe hancinansu da hankici, da sauran ƙyallayen da za su iya rage musu yajin iskar mai zafi.