Labarai

Ƴan Sandan Najeriya Sun Tsare Ɗan Ƙasar Togo, Kan Zargin Hallaka Wani Magini

Rundunar ƴan sandan jihar Edo, ta daƙume wani ɗan ƙasar Togo mai suna, Michael Agbalo, mai shekaru 35, bisa zarginsa da hallaka wani ɗan Najeriya, da ke gudanar da sana’ar hannu, a Jihar Edo.

Tun da farko, wanda ake zargin, ya nemi Umar da ya tallafa masa a Aikin Gini, inda kuma rashin fahimtar juna ya shiga cikin lamarin, wanda har ya kai ga rasa rai.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor, ya ce guda daga cikin waɗanda su ka shaida yadda lamarin ya auku, mai suna, Clement Obagbikoko ne, ya shigar da rahoton lamarin, ga Ofishin ƴan sanda na Etete, da ke Benin.

Obagbikoko ya ce, bayan wanda ake zargin ya buƙaci ya taya shi Aikin ginin ne, shi kuma sai ya ƙaro wani mutum guda, da nufin ya taya shi.

“Bayan sun kammala kuma sai ya biya shi kuɗin Aikinsa, kuma ya tambayi ina na Umar, Inda ya ce masa ya tafi, tun lokacin da Matar mai aikin ta ke sanya ido a kai, da misalin ƙarfe 7 na Almuru.

“Nan da nan kuma mu ka buƙaci makashin da ya dawo gida, Inda aka kama shi”, a cewar sa.

Kakakin rundunar ƴan sandan, ya kuma ce wanda ake zargin, ya yi amfani da guduma ne wajen hallaka mamacin, kafin garzayawa da shi zuwa Asibiti. Ya kuma ce za su gurfanar da shi a gaban Kuliya, nan kusa.

A ya yin zantawarsu da Manema Labarai, shi ma wanda ake zargin, ya ce ya tuntuɓi Umar ɗin ne domin agaza masa a Aiki, amma daga ƙarshe ya hallaka shi, sakamakon rashin fahimtar juna.

Ya na mai cewa, “Bayan mun gama Aikinmu, sai nace ya wanke kayan Aikin, Amma ya ce ba zai yi ba, inda mu ka fara sa in sa. Ya kuma ɗauko Adda, inda ni na buge shi a kansa da guduma, sakamakon farmakin da ya kawo min da Addar”.

“Bayan na buga masa kuma, ya faɗi ƙasa, kuma a nan na bar shi. Amma na yi nadamar buga masa gudumar, bayan da ya mutu yanzu”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button