Tsaro

Ƴan Sandan Nasarawa Sun Yi Ram Ɓarawon Da Ya Addabi Karu

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, ta samu nasarar daƙume fitaccen ɓarawon da ake zargi da addabar ƙaramar hukumar Karu, da sace-sace.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, shi ne ya bayyana hakan, ta cikin wani jawabi da aka rabawa Manema labarai, ranar Alhamis, a Lafia.

Inda ya ce, wanda ake zargin da ma ya daɗe a cikin komar ƴan sanda, kuma a yanzu ne su ka samu nasarar daƙume shi, a babban birnin tarayya Abuja, bayan namijin ƙoƙarin da Jami’ansu su ka yi.

Jawabin na cewa, ”A ranar 27/03/2023, da misalin ƙarfe 12:30 na rana ne, aka shigar da ƙorafi a ofishinmu da ke Karshi, a ƙaramar hukumar Karu, game da satar kayayyakin gida, da su ka haɗarda Mota ƙirar Toyota Matrix 2010.

”Kuma bayan karɓar ƙorafin ne, sai aka ƙaddamar da bincike. Inda rundunar ƴan sanda ta samu nasarar kama wanda ake zargi da addabar yankin da sace-sace, a ranar 28 ga watan Maris, na 2023, a Jikwoyi, da ke babban birnin tarayya Abuja. Wani matashi ne mai suna, Gabriel Okpe, mai shekaru 32.

”Bayan kama shi kuma, mun samu motoci da su ka haɗarda ƙirar Toyota matrix, mai lamba ABC 277 FV Abuja; sai Honda Accord, mai lamba LC 699 EKY Lagos, da Talabijin ɗin bango guda biyu; sai injin Janareto guda; Sai Fankar ƙasa; Da Computer Laptop; sai Microwave; Gas Cylinder da Burner; da IPads biyu; da kuma waya ƙirar Samsung, da sauran kayayyaki”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button