Ƴan Vigilante Sun Hallaka Ƙasurgumin Ɗan Bindigar Da Ya Addabi Jihar Kebbi
Rahotanni sun bayyana yadda Jami’an rundunar tsaro ta Vigilante su ka samu nasarar hallaka wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, a yankin ƙananan hukumomin Bunza da Kalgo, da ke jihar Kebbi, Dogo Oro, a ƙauyen Tunga, da ke mazaɓar Tilli, ta ƙaramar hukumar Bunza.
Babban Sakataren yaɗa labaran Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Ahmed Idris, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani jawabi da ya gabatar ga Manema Labarai, ranar Juma’a, a birnin Kebbi.
Shi ma, Daraktan tsaron jihar, AbdulRahman Usman, ya tabbatar da lamarin, ya yin da ya ke jawabi kan halin da sha’anin tsaro ya ke ciki a jihar.
Usman ya ce, “Ɗan bindigar ya zo ya na hantarar mutane da safiyar yau, ɗauke da makamai, inda Jami’an Vigilante su ka yi masa kwanta-kwanta su ka hallaka shi.
“Sanusi Ibrahim-Geza, wanda shi ne shugaban rundunar tsaro ta Vigilante, a jihar Kebbi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, a safiyar Juma’a, inda ya ce Kwamandan rundunar na ƙaramar hukumar Bunza, C/SUV Faruku Mashayabo ne, ya jagoranci aikin”.
Usman ya kuma ce, kyakykyawan aikin da Jami’an rundunar ta Vigilante su ke gudanarwa, ya na ƙara ƙarfafa musu gwuiwa, “Domin kuwa mutanenmu za su zauna ƙalau, a gidaje da ƙauyukansu, za kuma su gudanar da kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali, musamman ma a yankin Kanzanna.