Wasanni

Ƴan Wasan Super Falcons 7 Na Takarar Zama Gwarazan CAF

Aƙalla ƴan wasan tawagar Najeriya ta Super Falcons bakwai ne ke neman rabauta da kyautar gwarazan ƴan wasa na CAF a wannan shekarar.

Jadawalin ƴan wasan, ya ƙunshi ɗumbin ƴan wasan Najeriya da su ka haɗar da, Asisat Oshoala, Chiamaka Nnadozie, Rasheedat Ajibade, Toni Payne, Christy Ucheibe, Osinachi Ohale, har ma da yar wasa, Uchenna Kanu.

Kakar wasanni ta wannan shekarar dai, ta kasance abar tunawa ga tawagar ta Super Falcons, bayan da ta samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen ƴan 16 a gasar Kofin Mata ta duniya, da ake gudanarwa a ƙasashen Australia da New Zealand.

Sai da tawagar ta kusa samun cancantar zuwa wasan daf da na kusa da na ƙarshe a wasan, kafin a cireta a bugun fenareti, ya yin wasan da su ka fafata da tawagar ƙasar Ingila.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button