Ilimi

Ɗalibai Masu Ƙaramin Ƙarfi Ba Za Su Amfana Da Bashin Ɗalibai Ba – ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU), ta bayyana cewar ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi da ƴan asalin Najeriya ba za su amfana da tsarin bayar da bashin ɗalibai na Gwamnatin tarayya ba, sakamakon ire-iren ƙa’idojin da ke tattare da karɓar bashin.

Shugaban ASUU reshen Jami’ar Jos, Dr Mwolwus Jurbe, shi ne ya bayyana hakan, ya yin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, ranar Asabar, a birnin Jos, ya na mai cewar, ire-iren tsare-tsaren da aka sanya kafin karɓar bashin ba su yi dai-dai da abin da ƴaƴan talakawa za su iya cikawa ba, wanda kuma domin su ne aka fito da tsarin bada lamunin.

NAN, ya rawaito yadda, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaɓa hannu kan dokar bada bashin ga ɗaliban ƙasar nan ta shekarar 2023, tun a watan Yunin wannan shekara.

Dokar dai, ta yi tanadin bayar da bashi marar ruwa ga ɗaliban da ke Karatu a Manyan Makarantun gaba da Sakandire na ƙasar nan.

Wasu daga cikin sharuɗɗan da aka sanya kafin rabauta da bashin sun haɗarda: Samun gurbin karatu a guda daga cikin Jami’o’in Gwamnati, ko Kwalejojin Fasaha (Polytechics); Kwalejojin Ilimi (COE), ko Cibiyar bayar da horo kan ƙwarewa ta musamman a fannonin dogaro da kai (TVET).

Ka zalika wajibi ne, abin da Iyalin da Ɗalibin ya fito su ke iya samu a wata ya kasance bai haura 500,000 ba a shekara guda, tare da gabatar da Ma’aikatan Gwamnati guda biyu, a matsayin masu tsaya masa (Guarantors).

Wajibi ne kuma, masu tsayawa Ɗalibin su kasance aƙalla Ma’aikatan Gwamnatin da su ka kai Matakin Albashi na 12, ko Lauyan da ya shafe tsawon shekaru 10 a fagen shari’a.

Dukkannin ɗaliban da aka taɓa samu da laifin satar jarrabawa, ko shayen miyagun ƙwayoyi su ma basu cancanci samun wannan bashi ba.

Bugu da ƙari, dokar ta yi tanadin fara biyan wannan bashi, shekaru biyu bayan kammala Hidimar Ƙasa (NYSC), kuma za a dinga ɗaukar kuɗin ne daga Albashin wanda ya amfana da wannan shiri, ta hanyar cire kaso 10.

Su ma waɗanda su ke gudanar da Sana’o’in dogaro da kai, za su dinga biyan kaso 10 ne, na abin da su ke iya samu a wata.

Sai dai, ASUU ta buƙaci Gwamnati da ta sassauta lamarin, ta yadda kowanne ɗalibi zai iya amfana da shirin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button