Labarai

Ɗaliban Ƙasar nan Da ke Maƙale A Sudan, Na Kan Hanyar Dawowa

Alamu na bayyana yiwuwar dawowar wani adadi na jama’ar ƙasar nan, da ke maƙale a ƙasar Sudan, sakamakon hargitsin da ke cigaba da gudana a ƙasar, a yau (Laraba).

Hukumomin ƙasar nan dai, sun gaza bayyana tartibiyar rana, ko lokacin dawowar ɗaliban. Sai dai, wani cigaba da aka samu a iyakar Egypt da Port Sudan na bayyana yiwuwar isowar rukunin farko na jama’ar zuwa Abuja, ko Lagos, a yau.

Ɗaliban waɗanda su ka bar Khartoum tun a ranar Larabar makon da ya gabata, sun maƙale ne a iyakar Misra, har tsawon kwanaki shida, kafin daga ƙarshe hukumomin ƙasar ta Egypt su basu damar tsallake iyakar, a ranar Litinin.

Hukumomin ƙasar ta Egypt dai, daman sun bayyana cewar za su bar jama’ar ta ƙasar nan su tsallake iyakarsu ne, bayan amincewa tare da sanya hannu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna.

Hakan ne kuma ya sanya manyan motocin da ke ɗauke da jama’ar ta ƙasar nan, su ka ci burki a gefen iyakar ta Misra, tare da cigaba da jiran tsammani.

Ɗaliban waɗanda ke Arqin sun ce a jiya dai an karɓi takardun tafiyarsu, a cigaba da shirye-shiryen da ake na tsundumarsu ƙasar ta Egypt.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button