Ɗaliban Da Su Ka Kammala Jami’ar Madonna Ne Kawai Su Ke Fita Da Budurcinsu – Jagora
Jagoran samar da Jami’ar Madonna, da ke Najeriya, Reverend Father Emmanuel Edeh, ya yi iƙirarin cewar, dukkannin ɗalibai matan da su ka shiga Jami’ar da budurcinsu, to babu shakka su na kammala makarantar da budurci, saboda tarbiyyar da ake cusa musu.
Edeh, ya bayyana hakan ne, ta cikin wani faifan bidiyo da tashar talabijin ta Channels ta wallafa, a ranar Laraba, ya yin da ya ke bayyana yadda Jami’ar ta mayar da hankali kan inganta tarbiyya da kyawawan ɗabi’un ɗalibanta.
Jagoran, ya kuma ce, idan mutane daga ƙasashen ƙetare su ka je wurinsa su na neman Aurar cikakkiyar budurwar da ke tare da budurcinta, to babu shakka zai sanar da su cewar, hanya guda ta samun hakan kawai shi ne zuwa Jami’ar Madonna.
Ya ce, “Madonna Jami’a ce da babu ƙungiyoyin asiri, aikata rashin tarbiyya, satar jarrabawa, cin zarafi, kuma bama amincewa da shan miyagun ƙwayoyi. Haka zalika ko kaɗan ba ma aminta da aikata zinace-zinace.
“A Jami’ar nan ne kawai, mu ke tabbatar da cewa, Matan da su ka shigo a matsayin ƴan mata, sun kammala a matsayin ƴan mata.
“Ku faɗa min, a duk faɗin duniya – wacce Jami’a ce za ta iya riƙe wannan kambun. Hakan ne yasa da zarar na haɗu da mutane daga London, Amurka, Burtaniya, ko Jamus, kuma su ka ce min su na son Aurar budurwa. Sai na ce musu to hanya ɗaya ta samun hakan, ita ce kawai zuwa Jami’ar Madonna”.