Nishaɗi
Ɗalibar OAU Ta Fara Gudanar Da Gasar Wanke Hannu Ta Sa’o’i 50, Domin Shiga Kundin Bajinta
Wata Ɗaliba mai suna, Subair Enitan, da ke karatu a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, a jihar Osun, ta fara gudanar da gasar wanke hannu a yau (Juma’a), domin neman shiga kundin bajinta na Guinness World Records, a matsayin wacce tafi kowa daɗewa ta na wanke hannu.
Ɗalibar dai, ta fara gudanar da aikin wanke hannun ne, a Sub car park, da ke Jami’ar ta OAU, Ile-Ife, a jihar Osun.
Enitan, na fatan shiga kundin bajinta na duniya ne, a matsayin wacce tafi kowa daɗewa tana wanke hannunta, har tsawon sa’o’i 50.
Zuwa lokacin da Rariya Online ta ke haɗa muku wannan rahoto kuma, Enitan ta shafe sama da sa’o’i bakwai, da fara wanke hannun nata.