Ilimi

Ɗalibin Da Ya Shafe Shekaru 54 Ya Na Karatun Digiri

Sama da ƙarni biyar bayan fara karatun Digirinsa na farko, a ƙarshe dai, Arthur Ross ya samu nasarar kammala karatunsa, daga Jami’ar British Columbia (UBC), a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Mr Ross, mai shekaru 71 a duniya, ya kasance ɗalibi mafi daɗewa ya na karatu, a tarihin Jami’ar da ya kammala.

Akwai yiwuwar ma ya kasance Ɗalibi mafi jinkirin karatu, a faɗin duniya. Duba da yadda ya shafe kimanin shekaru 54 ya na gudanar da karatunsa na Digirin farko, wanda hakan ya bashi damar shallake ɗalibin da sunansa ke cikin Littafin mutanen da su ka nuna bajinta na duniya (Guinness World), Robert FP Cronin, wanda ya fara karatun Digirinsa na farko, a fannin kimiyyar halittu masu rai (Biology), a Jami’ar Princeton, tun a shekarar 1948, inda kuma ya samu damar kammalawa a shekarar 2,000.

Ana ganin matsalar da ke haifar da samun ire-iren wannan jinkiri dai, bata rasa nasaba da rashin zaɓar fannonin karatun da su ka dace, da ma rashin mayar da kai.

Anan Najeriya kuwa, Ɗalibai na bayyana ɗaukar kwasa-kwasan aro (Subsides – Electives) a matsayin babban abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, inda a wasu lokutanma hakan ke zame musu ƙarfen-ƙafa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button