Ɗalibin Jami’a Ya Rasa Ransa, Kwana Guda Kafin Rubuta Jarrabawarsa Ta Ƙarshe
Wani Ɗalibin Aji 5, a Jami’ar Fasaha ta Tarayya, da ke Akure (Federal University Of Technology, Akure), Ayomide Akeredolu, ya rasa ransa, kwana guda kafin rubuta jarrabawarsa ta kammala Makarantar .
Hakan ne kuma, ya sanya Ɗaliban Makarantar su ka gudanar da zanga-zangar lumana, a jiya (Juma’a), da nufin nuna fushinsu kan rashin ingantattun kayayyakin kula da lafiya a Jami’ar, waɗanda su ke ganin da Makarantar ta mallake su, babu shakka Ɗalibin ba zai rasa ransa ba.
An dai ɗora Alhakin rasa ran ɗalibin kacokan ne akan rashin Ingantattu kuma wadatattun kayayyakin kula da lafiya, a Cibiyar lura da lafiya ta Jami’ar (University’s Health Centre).
Tun da farko, Abokanan karatun, Ayomide Akeredolu ɗin ne dai, su ka garzaya da shi zuwa Asibitin Makarantar, a daren Alhamis, bayan da ya yanke jiki ya faɗi a ɗakinsa.
Sai dai, hukumomin gudanarwar Jami’ar sun ce daman tuni Ɗalibin ya rasa ransa, tun kafin ƙarasawa da shi Asibitin.
Kuma zanga-zangar lumanar da Ɗaliban Makarantar su ka gudanar a ranar Juma’a, ta haifar da rufe hanyar Akure zuwa Ilesa ga Ababen Hawa, na tsawon sa’o’i.
“Ɗalibin ya yanke jiki ya faɗi ne a ɗakin kwanansa (Hostel), Kuma nan da nan aka garzaya da shi zuwa Asibitin Makaranta”, a cewar guda daga cikin masu zanga-zangar, Wanda ya gaza bayyana Sunansa.
“Kuma ya rasa ransa a Asibitin, Saboda rashin kayayyakin kula da lafiya.
“Mun je da Ɗalibin Asibitin ne, da misalin ƙarfe 8:30 na dare. Da mu ka je kuma, sai muka tarar babu wutar lantarki, kuma babu iskar Oxygen ma da za a shaƙa masa. Sai fitulunmu muka dinga haskawa”.
Inda ya kuma ƙara da cewar akwai wani Ɗalibin ma, da Cibiyar kula da lafiyar ta gaza bashi kulawa, a ranar Alhamis, duk da halin buƙatar kulawar gaggawar da ya ke ciki, kawai saboda bai je da ID Card ɗinsa ba.
Da ta ke martani kan wannan lamari, Hukumar gudanarwar Jami’ar, ta amince da cewar Asibitocin Makarantar su na fama da ƙalubale, sai dai ta sha alwashin gyarawa.