Siyasa

Ɗan Takarar Gwamnan Taraba Na Jam’iyyar NNPP, Zai Garzaya Gaban Kotun Ƙoli

Ɗan takarar Gwamnan jihar Taraba, na jam’iyyar NNPP, a zaɓen da ya gabata, Farfesa Sani Yahaya, ya yi watsi da hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta yanke, na korar ƙarar da ya ɗaukaka, ya na ƙalubalantar nasarar Gwamna Kefas Agbu.

Kotun ɗaukaka ƙarar dai, ta kori ƙarar da Ɗan takarar Gwamnan NNPP ɗin ya shigar gabanta ne, ya na ƙalubalantar hukuncin Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar, wanda ya bawa Kefas Agbu nasara.

Da ya ke martani kan hukuncin, a jiya, ya ce zai garzaya gaban Kotun ƙoli, domin ƙwato nasarar zaɓarsa da al’ummar jihar su ka yi.

Yahaya ya ce, sam babu Adalci, a dukkannin hukunce-hukuncen Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan, da ta Ɗaukaka Ƙarar, waɗanda su ka kori ƙorafin da ya shigar, ya na mai cewar, “Dukkannin hukunce-hukuncen guda biyu, yunƙurin gurgunta fannin shari’a ne, da kuma tsantsar rashin adalci.

Farfesa Yahaya, ya ce shi da Lauyoyinsa, sun yi mamaki matuƙa kan yadda Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ƙorafin da ya shigar gabanta, bayan rasa wasu fejika guda 8 waɗanda ke cikin hukuncin da Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta yanke.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button