2024: Saudiyya Ta Bawa Najeriya Gurbin Mahajjata 95,000
Maáikatar Aikin Hajji ta ƙasar Saudi Arabiá, ta amince da bawa ƙasar nan gurbin Mahajjata 95,000, a ya yin Aikin Hajji na shekarar 2024, da ke tafe.
An kuma bayyana amincewa da hakan ne a ya yin taron da hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON, ta gudanar ta Allon gani-gaka da Maáikatar Hajji Da Umrah ɗin, a jiya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewar, taron wanda ya ke alamta farkon shirye-shiryen Aikin Hajji na shekarar 2024, ya samu halartar Shugaban Kwamitin Aikin Hajji, Jafar Mohammed, sai wakilin shugaban kwamitin majalissar dattijai kan alámuran ƙasashen ƙetare, Sanata Abubakar Sani Bello, da Jakadan Najeriya a Saudiyya, Bello Abdulƙadir.
Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wani jawabi da Mataimakin Daraktan yaɗa labaran hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki, ya fitar a jiya.
Ana kuma sa ran ƙasar nan, za ta kammala dukkannin shirye-shiryenta game da samar da abinci, masaukai, da ma sufuri, nan da kwanaki 120.