Siyasa

Abba Gida-Gida Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Karɓar Mulki

Da yammacin ranar Asabar ne, sabon zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, mai laƙabin ‘Abba Gida-Gida’, ya ƙaddamar da kwamitin karɓar mulki, daga Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, mai barin gado, bayan da ya fitar da sunan shugaba, da membobin kwamitin tun a ranar Juma’a.

Jerin sunayen membobin kwamitin kimanin 65 dai, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran zaɓaɓɓen Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu.

Inda sunayen su ka haɗar da, Sanata Abdullahi Baffa Bichi, a matsayin shugaban kwamitin; sai membobi da su ka haɗarda: Tsohon Mataimakin Gwamna, Farfesa Hafiz Abubakar; Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, reshen jihar Kano, Shehu Wada Sagagi; Shugaban Jam’iyyar NNPP, reshen Kano, Umar Haruna Doguwa; Ahmad Garba Bichi; Shugaban Kwamitin yaƙin neman zaɓe, Dr Ali Haruna Makoɗa; Barista Maliki Kuliya; Barista Haruna Isa Dederi; Dr Ɗanyaro Ali Yakasai; Injiniya Muhammad Diggol; Dr Ibrahim Jibrin Provost; Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa; Dr. Labaran Abubakar Yusuf; Farfesa Sani Lawan Malumfashi; Alhaji Umar S. Minjibir; Dr. Ɗanjuma Mahmud; Injiniya Kabir Jibrin; Dr. Farouk Kurawa; Injiniya Dr. Marwan Ahmad; Dr. Aminu Garba Magashi; Alhaji Aminu Ibrahim Abba; Alhaji Laminu Rabi’u; Injiniya Bello Muhd Ƙiru; Injiniya Garba Ahmed Bichi; Tajudeen Othman; Sadiya Abdu Bichi; Yusuf Jamo; Nura Ɗankadai; Alhaji Yusuf Lawan; da Umar Maggi Gama.

Sauran su ne: Hajiya Azumi Namadi Bebeji; Farfesa Auwalu Arzai; Rayit Honorable Gambo Sallau; Shugaban kwamitin tattara bayanan sirri, Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado; Shugaban ƙungiyar ƙwadago na jihar Kano (NLC); Shugaban KACCIMA na jiha; Alhaji Audu Kirare; PS Adda’u Kutama; PS Aminu Rabo; Alhaji Sule Chamba Fagge; Alhaji Usman Adamu Gaya; Injiniya Tijjani Yunkus; Injiniya Abubakar Argungu; Alhaji Yahaya Musa; Rayit Honorabil Alasan Kibiya; Farfesa Ɗahiru Sani Shuaibu; Arc. Ibrahim Yakubu; Dr Kabiru Muhd Kofa; Dr. Mustapha Sani; Sheikh Malam Abbas Abubakar Daneji; Barista Bashir Yusuf Mohd; Barista Ibrahim Wangida; Umaru Idi; Dr. Sulaiman Wali; Rabiu Liliko Gwarzo; Alhaji Kabiru Gwarzo; Hajiya Aisha Kaita; Hajiya Aisha Lawan Saji; Ali Yahuza Gano; Auwal Mukhtar Bichi; Alhaji Musa Fagge; Wakili Aliyu Garko; Tukur Bala Sagagi; Sai Dr Nura Yaro Dawakin Tofa; da PS Abdullahi Musa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button