SiyasaUncategorized

Abba Gida-Gida Ya Rantsar Da Masu Bashi Shawara Na Musamman

Abba Gida-Gida Ya Rantsar Da Masu Bashi Shawara Na Musamma

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da masu bashi shawara na musamman (SSA’s) guda 45, inda ya buƙaci da su kasance masu ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora musu.

An gudanar da bikin rantsar da masu bada shawarwarin ne dai Yau (Alhamis), a fadar Gwamnatin Kano.

Gwamnan ya ce, ya zaɓo su ne bayan duba cancanta, Aiki tuƙuru, da ma kamanta gaskiyarsu, wanda hakan ya sanya ya ke da ƙwarin guiwa akansu.

Ya kuma sanar da su cewar, Al’ummar Jihar Kano su na matuƙar tsammanin abubuwan alkairi da dama daga wannan Gwamnati tasu, a don haka akwai buƙatar su kasance masu nin-ninka ƙwazon da aka sansu da shi.

Ka zalika, ya yabawa ƙungiyar ƙwadago ta NLC reshen Jihar, bisa haɗin kan da ta ke bawa Gwamnatinsa.

Inda a ƙarshe, ya buƙaci sababbin masu bashi shawarar da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan ƙwadago, dan cimma muradan Gwamnatinsu.

A baya-bayan nan ne dai, Gwamnan na Kano ya naɗa sababbin masu taimaka masa na musamman kimanin 72, da masu kawo rahotanni na musamman guda 44, sai masu bashi shawara na musamman 14, wanda ya samar da Jimillar 130.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button