Ilimi

ABUBUWA 6 DA YA KAMATA ƊALIBAN JAMB SU YI LA’AKARI DA SU, KAFIN ZAƁAR MAKARANTA

Mafi yawa daga cikin ɗaliban da ke rijistar jarrabawar JAMB UTME, su na halartar cibiyoyin rijista ne, ba tare da sanin haƙiƙanin makarantun da ya kamata su sanya a matsayin zaɓukansu (choices) ba. Hakan ya sa mu ka yi nazari, tare da wallafa muku wasu abubuwa shida, da ya kamata a ce kun yi la’akari da su, kafin zaɓar kowacce makaranta, a matsayin wacce ku ke muradin yin karatu a ciki.

Yin zaɓin ƙwarai ta fuskar makarantun da ake son yin karatu a ciki, ko akasin hakan, na taka gagarumar rawa, a cikin sha’anin samun guraben karatu (Admissions), da ma bayan kammala karatun.

Ga Jerin Abubuwan Da Ya Kamata Ku Lura Da Su Kafin Zaɓar Kowacce Irin Makaranta :

1• Ku tabbatar an tantance makarantar, tare da course ɗin da ku ke son karantawa :

Wannan ita ce gaɓa mafi muhimmanci, a ya yin da ake yunƙurin zaɓar Makaranta, ko Jami’ar da ake muradin yin karatu, domin kuwa akwai Jami’o’i da Makarantu da dama da su ke karantar da wasu kwasa-kwasai, ba tare da sahalewar hukumar NUC, ko sauran hukumomin da ke da alhakin tantancewa ba. Saboda haka ku tabbatar NUC ta tantance Course ɗin da ku ke son karantawa a Jami’ar da ku ke da muradi, domin karantar wani Course ba tare da tantance shi ba, dai-dai ya ke da ɓata lokaci.

2• Cathment Area Na Makarantar :

Ya na da kyau ku san Cathment Area na dukkannin wata Makaranta, ko Jami’ar da ku ke son cikewa, domin kuwa catchment area ne, zai nuna muku sauƙin yiwuwar samun Admission ɗinku a wannan makarantar, ko akasin haka, duba da cewar, kowacce makaranta ta na ɗaukar kaso mafi tsoka na ɗalibanta ne, a yankunan da ke matsayin cathment areas ɗinta. Misali : Babbar Cathment Area ɗin Jami’ar Bayero, ita ce Kano, saboda haka dukkannin ɗaliban da su ka nemi gurbin karatu a Jami’ar daga Kano samun Admission zai fi musu sauƙi, fiye da wanda ya nemeta daga Ekiti.

Ku Lura : Ba wai muna nufin ka da ɗalibi ya nemi Jami’ar da ba ta cikin cathment area ɗinsa bane, a’a kawai dai mun bayyana irin rawar da cathment area ta ke takawa ne, wajen samun gurbin karatu (Admission) cikin sauƙi, da irin fifikon da makarantun su ke bawa Ɗaliban jihohinsu.

3• Sanin Tarihin Yawan Tsundumar Makarantar Yajin Aiki :

Ba ya ga Yajin Aikin al’ada, da ƙungiyoyin ASUU da ASUP su ka saba shiga, lokaci bayan lokaci, akwai makarantun da su ka yi shura wajen shiga Yajin Aikin cikin gida, wanda hakan ke kawo tasgaro ga karatun Ɗalibansu, tare da tsawaita musu zaman gida. Saboda haka fahimtar ko makarantar da ka ke son nema ta na yawan tsunduma Yajin Aikin cikin gida, muhimmin abu ne, gabanin neman gurbin karatu a cikinta.

4• Abin Da Makarantar Ta Ke Buƙata Kafin Bada Admission :

Sanin kowa ne, makarantun Najeriya su na da mabanbantan abubuwan da su ke buƙata a kowacce gaɓa ga Ɗaliban da su ke nemansu, kafin basu guraben karatu, saboda haka ya na da kyau ku lura da abin da su ke buƙata, tare da auna kanku a mizanin cika ƙa’idojin nasu, kafin nema. Misali: wasu makarantun su na karɓar maki 200 ne a matsayin minimum Cut-Off mark; ya yin da wasu su ke karɓar maki 160 (za ku iya kwatanta abin da za su buƙata ne, ta hanyar duba Admission requirements ɗinsu na shekarar da ta gabata).

5• Ka fahimci tsarin Screening na makarantar :

Wasu daga cikin Makarantu, su na tantance sakamakon kammala Sakandire (O’Level Result) ɗin ɗalibi ne kawai, sai su bashi Admission (bayan ya kai Cut-Off mark ɗinsu), ya yin da wasu kuwa su ke gudanar da jarrabawar Post-UTME (Aptitude Test). Kun ga kenan, a wasu makarantun samun kyakykyawan sakamakon O’Level kawai ya wadatar a baka Admission, ya yin da a wasu kuwa, lamarin ya sha ban-ban.

6• Tsadar kuɗin makarantar :

Nasan ɗaliban da ke karanta wannan rubutu ganau ne, kan yadda tsadar kuɗaɗen Registration, ya raba ɗalibai da dama da makarantunsu, a kakar karatun da ta gabata, saboda haka akwai buƙatar ɗalibi ya binciki tsadar kuɗin registration na makarantar da ya ke son cikewa, dan ganin ko zai iya biya, ko akasin haka. Idan ya fuskanci kuɗin ya fi ƙarfinsa, sai ya sauya tunani zuwa wata makaratar.

DOMIN TAMBAYA, KO NEMAN SHIGA ASOF JAMB GROUP, KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR : 08039411956.

Rubutawa : Miftahu Ahmad Panda.

08039411956.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button