Ilimi

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Lura Da Su, Gabanin Rubuta Jarrabawar Mock A Ranar Alhamis

Tuni aka fara cire Slip ɗin jarrabawar gwaji ta Mock, da hukumar JAMB ta tsara gudanarwa a ranar Alhamis ɗin makon da mu ke ciki, 7 ga watan Maris.

Dukkannin ɗalibin da ya bayyana sha’awarsa ta rubuta Jarrabawar, tun a ya yin rijistar JAMB, zai iya halartar adireshin: https://slipsprinting.jamb.gov.ng/printmockexaminationslip, domin cire Slip ɗinsa, ta hanyar sanya registration number ɗinsa ko adireshin Email, tare da danna maɓullin “Print Examination Slip”.

Bayan cire Slip ɗin kuma, ɗalibi zai samu rana, lokaci, da kuma wurin da zai rubuta jarrabawarsa, dukka a jikin slip ɗin, har ma da lambar wurin zama (Sit Number).

Mock, jarrabawa ce da ake rubutawa a Na’ura Mai Ƙwaƙwalwa, kamar yadda ake rubuta jarrabawar JAMB, kuma ita ma akan rubuta darussa huɗu ne (Four Subjects).

Ita ma Mock, ta na da maki 400 ne kamar JAMB, sai dai ba a amfani da shi wajen neman Admission, kawai dai auna fahimta ne, tare da ƙara fahimtar yadda jarrabawar JAMB take, gabanin tunkarar UTME.

KU SANI: Ba a shiga da Agogo, Waya, Zobe, ATM, Jaka da makamantansu cikin ɗakin rubuta Jarrabawar Mock.

ALLAH YA BADA NASARA

Rubutawar: Miftahu Ahmad Panda

08039411956

tare da biyan

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button